home . about . others
DA SAURAN KALLO (Part I)
11-03-21 (00:12)


*T* a shigo gidan nasu hannunta riq'eda wata 'yar q'aramar baby nokia tana waya, kaida kaga yanayin halin da nokiar take ciki kasan ta fara jin jiki dan har da wata 'yar siririyar farar salatif aka nad'e a q'asan ta dashi a wajen sa cajin kenan da wani d'an falan day'a na salatif d'in gudun kada wajen ya ida su6utowa yayo qasa.

amman inkaji yanda heenduh ke faman sake nonnoq'e sanyayyar murya tata tana magana harda wani lumshe idanunta zaka d'auka wata iriyar babbar touching ce take wayar da ita, wannan karan a tsiwace take fad'in "mtsss haba dan Allah nace ka bari sai next week zamu had'u anan gida dan wlh kokazo yanzun kayi wahalar banza danba wai fitowa zanyi ba uniform d'ina zan goge danma kaji fah, haba ka fiye naci musaddiq wallahi"

daga can 6angaren day'a musadiq ya dafe kansa ya rasa miyasa yarinyar nan ke son had'a masa hyper tention ba da sonta a ransa kamar zuciyarsa zata tsinke yakeji, da q'yar ya bud'e bakinsa yace "to.. to shiknn gimbiya ta heenduh Allah shi kaimu juma'ar lpia ai kmr gobe ne inda saura kwana 2 ko nikeji? " tana tsoki ta katse wayar take fad'in "ban sani ba nataccen mutum kawai" tana mgnr amman still hankalin ta na kan wayar tana tafiya dan qarasawa cikin gidan nasu, da yake babu zaure a gidan bika wuce ne.

turo lips d'in bakinta tayi hakan ne kuma ya bawa qwan zuma cwingum d'in dake maq'ale cikin bakinta da yayi q'atoto damar fitowa ya fashe sannan ta cigaba da rats rats tana cigaba da sakin qarar q'wan cwingum din a bakinta abinda babanta ya hanata kuma knn wato qas qas na cwingum indai yana gida kuwa bata yarda ma ta fara sa cwingum a bakinta saiya fita dan ita kam sam sam batta iya taunar cwingum batareda da tai masa qwai da q'as q'as ba, tana shirin d'agowa da fuskarta kenan daga saman wayar tata sakamakon sanin jarababben qamshin mutumin da tasan waye mamallakin turaren da tayi. bata ankara ba kuwa by mistake taji goshinta ya doki gefen chest dinsa, da sauri ta ware masa manyan fararen q'al d'in idanunta a kansa fuskarta cike da mamakin miya kawosa gidansu bayan abinda ya faru jia tsakanin babanta da nasa dud akansa kuma? ranta taji yayi wani mugu mugun 6aci sosai, nan ta sake ware masa manyan idanun nata akansa bayan ta soke wayar tata a cikin bra d'inta daga saman rigarta ta atamfa wacce ta fara jin jiki.

matsowa tayi da sauri a gabansa ganin yanda yake shirin zagaye ta ya wuce bayan gama binta da kallon banza da ya gama yi shima harda wani ta6e red lips dinsa yayi bayan ya kakka6e gefen farar rigar sa ta t -shert da wani blue hankicerf dinsa cike da qyanqyamin abun, wato a dai dai inda kanta ya d'an gogi qirjin nasa.

cak yaja ya tsaya shima ganin yanda tasha gabansa da sauri hannuwanta na saman kwankwaminta tana binsa da wata iriyar muguwar harara a tsiwace tace "miya kuma sake kawo ka gidanmu eye d'an masu kud'i?
0 comment of posting DA SAURAN KALLO (Part I)
38

no comment
» DA SAURAN KALLO (Part I)
» fasebook Blog Post
» Fnsdfghdfvnm
Name:

Comment:

Smilies List
online: 0 | hits: 299x
© pvlcms